Kuma dai: Wani mutum ya mutu sakamakon cutarcoronavirus a jihar Lagos

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin jahar Lagas a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, ta tabbatar da mutuwar wani mara lafiya sakamakon cutar coronavirus a jahar. Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi, wanda ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya ce a yanzu mutane biyar kenan suka mutu a jahar.

Ya ce mutumin ya rasu ne sakamakon tabarbarewar lafiya da ke da nasaba da coronavirus. Abayomi ya kara da cewa an samu sabbin mutane 11 da suka kamu a ranar Asabar.

A yanzu jahar na da jimlar mutane 177 da suka kamu da COVID-19. Kwamishinan ya ce jahar ta sallami mutane 50 da suka warke. “An samu sabbin mutane 11 da suka kamu da COVID-19 a Lagas a ranar 11 ga watan Afrilu, 2020.

Gaba daya wadanda suka kamu a jahar Lagas sun kama 177. “Labari mai dadi shine cewa an sallami sabbin mutane hudu da suka warke.

 “A yanzu haka an sallami jimlar mutane 50. Abun bakin ciki, an sake samun wanda ya mutu a Lagas inda suka zama mutane biyar. “Don haka muna bukatar mutane da su yi gwajin COVID-19 da wuri sannan a fara kula da mutum kan lokaci domin tsirar da rayuka.

 “A kira layin neman agaji na COVID-19 08000CORONA; domin kai rahoton duk wani lamari da ke da alaka da COVID-19,” in ji shi. A wani labarin kuma, mun ji cewa an samu tashin hankali a jihar Anambara yayinda aka nemi mutumin farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar aka rasa.

 Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar ranar Juma'a cewa an tabbatar da bullar cutar ta COVID-19 a jihar.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN