Gwamnatin jihar Niger ta bayar da umarnin kama wani Kansila bisa zargin tserewa da buhu 30 na masara da aka tanada domin taimakon bayin Allah sakamakon matsalar coronavirus.
Sakataren Gwammnatin jihar Niger kuma shugaban kwamitin harkar COVID-19 Alh. Ahmed Ibrahim Matane ya saanar da haka. Ya ce Kansilan yana cikin kwamitin da aka sa domin raba wa jama'ar mazabarsa buhuhuwan masaran.
Sakataren Gwamnatin ya nuna rashin jin dadin kan abin da Kansilan ya yi, ya kuma cean sa jami'an tsaro su kama Kansilan.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari