El-rufai ya ce Almajirai daga jihar Kano ne suka sa yawan masu corovid-19 ya karu a Kaduna

Rahotun Legit Hausa

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufa'i ya ce sun samu karin mutum 19 masu dauke da cutar korona, al'amarin da ya kara yawan adadin masu cutar a jihar daga 9 zuwa 25.

Elrufa'i wanda ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Twitter ya ce an yi wa almajiran guda 40 gwaji inda sakamakon 19 daga cikinsu ya nuna suna dauke da cutar ta korona.

Gwamna Elrufa'i ya kuma kara da cewa yanzu ta tabbata shigi da fici da ake yi wa jihar tasa ne ke janyo karuwa masu cutar a Kaduna, inda ya ja hankalin jami'an tsaro da su ci gaba da sanya ido kan duk masu shiga birnin ta barauniyar hanya.

Ko a makon da ya gabata ma sai da gwamnan ya sanar cewa sun samu biyar daga cikin almajiran da aka mayar wa jihar tasa daga Kano masu dauke da cutar.

A kokarin dakile bazuwar cutar korona a birnin Kano ne dai ya sa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya fito da shirin mayar da almajirai jihohinsu na asali.

Da dama masana harkar lafiya sun soki shirin bisa dogaro da cewa hakan ka iya fantsama cutar a wasu jihohin da ba su da ita.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN