Coronavirus: Gwamnan jihar Bauchi ya sami lafiya, ya halarci Sallar Juma'a

Rahotun Legit Hausa

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a ranar Juma'a ya halarci sallar jami'i. Hakan ya faru ne bayan sa'o'i kadan da aka sallamo shi daga cibiyar killacewa ta jihar sakamakon warkewa da yayi daga cutar coronavirus.

Gwamnan tare da mataimakinsa, Sanata Baba Tela, kwamishinoni, manyan jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya sun yi jami'i tare da dubban al'ummar Musulmi. Sallar Juma'ar da aka yi a babban masallacin jihar Bauchin ta zama ta farko da aka ga gwamnan a cikin jama'a tun bayan da aka tabbatar da ya kamu da cutar.

Sai dai kuma ya ki yin hannu da jama'a kamar yadda ya saba bayan tashi sallar Juma'a din, jaridar Daily Trust ta ruwaito. An sallama Gwamna Mohammed ne bayan gwaji na biyun da aka yi mishi ya tabbatar da cewa ya warke sarai. Kwamishinan lafiyan jihar, Dr Aliyu Muhammed Maigoro ya ce an sallami gwamnan ne bayan samfur biyu na jininsa sun nuna ya warke.

 "A yau Alhamis ne muke sallamar mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a jihar nan. Ya kasance a cibiyar killacewar na makonni biyu", a cewarsa.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyanawa duniya cewa ya samu waraka daga cutar Coronavirus bayan gwaji na biyu da aka yi masa. Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita da yammacin Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2020. Yace:

"Alhamdulillah. Yanzu na samu labarin. Gwaji na biyu da aka yi mun ya nuna cewa na warke. Ina godiya gareku gaba daya bisa addu'o'inku da goyon baya yayinda nike killace".

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN