Coronavirus: Direba mai dauke da cutar ya gudu daga inda aka killace shi a Minna

Rahotun Legit Hausa

Wani direban motan haya da ya kamu da cutar Coronavirus ya gudu daga inda aka killaceshi a garin Bida, jihar Neja kuma na bazama nemansa yanzu. Kwamishanan kiwon lafiyan jihar,

Dakta Mohammed Makunsidi, ya alanta nemansa ruwa a jallo kuma gwamnati ta nada kwamiti na musamman domin nemoshi. Yayinda yake jawabi ga manema labarai jiya a Minna, Makunsidi yace: "Mun yi mamakin guduwarsa kuma yadda ya gudu daga asibitin abin mamaki ne garemu har yanzu amma an harzuka wajen kamoshi."

"Mun samu labarin cewa ya gudu cikin Bida, kuma muna biye da shi yanzu. Mambobin hukumar yaki da COVID-19 da jami'an ma'aikatar lafiya na Bida yanzu domin nemansa da kuma tabbatar da cewa ya yi abinda cibiyar NCDC ta umurcesa."

Kwamishanan ya kara da cewa an killace wasu mutane biyu da suka dawo daga kasar Birtaniya da Canada a garin Kontagora kuma ana gwada su." A bangare guda, Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi, a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, ya umurci jami’an tsaro da su bindige duk wanda ya dawo jahar sannan ya yi kokarin guduwa daga inda ake killace mutane.

Gwamnatin jahar a karshen makon da ya gabata ta yi umurnin gaggawan killace akalla mutane 37 da suka shigo jahar ta daji bayan gwamnatin jahar ta yi umurnin rufe iyakokinta. Gwamnatin jahar ta yi umurnin cewa a gaggauta rufe dukkanin iyakoki a jahar domin hana yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Gwamnan ya kara da cewar a bindige duk wani bako da ya dawo sannan ya yi kokarin guduwa daga cibiyar killace mutane wanda a nan ne za a dunga yi musu gwaji a kullun har tsawon kwanaki 14 biyo bayan barkewar annobar coronavirus

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN