Rahotun Jaridar Aminiya
A karo na farko a tarihi an yi fashin sallar Juma’a a birnin
Kano, abin da Kanawa da dama suka bayyana a matsayin bakon al’amari.
Hakan dai ya faru ne sakamakon ayyana dokar hana fita da gwamnatin
jihar Kano ta yi a yunkurinta na hana cutar coronavirus yaduwa.
Wani dattijo mai kimanin shekara 80, Alhaji Bashir Garba, ya ce a iya rayuwarsa bai taba ganin hakan ba.
“Ban taba ganin lokacin da aka ce ba a yi sallar Juma’a ba. Lamarin
babu dadi sai dai babu yadda mutum zai yi sai hakuri, tun da hukuma ce
ta yi umarni da hakan kuma sha’ani ne na kula da lafiya”, inji Alhaji
Bashir.
Shi ma Dokta Yahaya Tanko ya bayyana cewa bai taba ganin lokaci makamancin wannan ba a iya tsawon rayuwarsa ta shekara 71.
Sai
dai Shugaban Sashen Tarihi na Kwalejin Shari’ar Musulunci ta Aminu
Kano, Malam Kamal Muhammad, ya ce ko da yake a tarihi ba a taba samun
lokacin da gwamnati ta hana sallar Juma’a a birnin Kano ba, an taba
samun yanayin da aka gudanar da sallar a tsorace wanda ya janyo mutane
ba su fita ba.
“A shekarar 1953 a lokacin da aka yi wata rigima ta NEPU da NPC an yi
wata hatsaniya da ake kira Kano Riot, wadda ta janyo ba a yi Sallar
Juma’a kamar yadda aka saba ba saboda mutane da yawa ba su halarci
sallar ba suna jin tsoron yiwuwar barkewar rigima.
“Amma fa ba wai gwamnati ce ta yi umarnin hana fitowa sallar ba”. inji Malam Kamal.
Da karfe 10 na daren Alhamis ne dai dokar hana fitar da gwamanti
jihar Kano ta kafa ta fara aiki, lamarin da ya sa ba a fita zuwa
masallatan Juma’a ba.
A kasa da mako guda ne dai aka tabbatar da cewa mutane 21 sun kamu da cutar ta coronavirus a jihar Kano.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari