An kama mutumin da ya saci mahaifa bayan an haifi jariri

Rundunar yansandan jihar Ogun, ta kama wani mutum mai shekara 43 Joshua Abraham bisa zargin sace mahaifada bayan an haifi wani jariri.

A wata sanarwa da kakakin hukumar yansandan jihar ta fitar, Abinbola Oyeyemi ta ce an kama Abraham ne bayan wani kokee da Kakar Jaririn Rahila Zakara ta shigar wajen yansanda, in da shaida masu cewa an sace Mahaifar jariri da uwarsa ta haiafa.

Rahotannin yansanda sun ce Zaakara ta shaida wa yansanda a ofishinsu na Ibafo cewa, Abraham ya je Asibitin da aka haifi jaririn ne, sai ya gaya wa Unguwarzoma cewa shi ne mahaifin jaririn, kuma ya bukaci a bashi mahaifar uwar domin ya je ya binne.

Bisa tunanin cewa shi ne ainihin mahaifin jaririn, sai unguwarzomann ta ba Abraham mahaifan.

Abraham makwabcin Zakara ne, wacce ita ce Kakar jaririn.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN