An kama matashi bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu a shifin Facebook a Kano

Mahukunta a jihar Kano sun kama wani matashi mai suna Mubarak Bala bayan an shigar da  kara a kansa a Shelkwatan yansandan jihar Kano bisa zargin cin zarafin Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) 
Wani ofishin Lauyoyi a jihar Kano ne ya shigar  da karar Mubarak Bala wanda ke zaune a layin Masallaci Bilal a rukunin gidaje na Karkasawa a birnin Kano, bayan ya wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook wanda  Lauyoyin ke ganin cewa cin zarafin Manzon tsira ne kuma yunkuri na harzuka al'umma Musulmi domin su tunzura su daui doka a hannunsu.

Mubarak ya wallafa  a shafinsa na Facebook cewa " Babu banbanci tsakanin Annabi TB Joshua (S.A.W) da Muhammadu (A,S) na Saudiyya, gara ma namu na Najeriya bay ta'addanci". 

Wadannan kalamai tuni suka ja kace nace a shafukan sada zumunta a Arewacin Najeriya.



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN