Za mu yi amfani da jami'an tsaro wajen hana taron jama'a - FG

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta yi amfani da sojoji da 'yan sanda wajen tabbatar da cewa jama'a sun nesanta da junansu domin takaita yaduwar kwayar cutar coronavirus.

Minista yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawarsa da manema labarai a Abuja ranar Litinin. Ministan ya ga baiken wasu jagorori da malaman addinai da suka yanke shawarar yin watsi da umarnin gwamnatin tarayya na hana taron jama'a masu yawa.

Wasu masallatai da coci-coci sun gudanar da taron ibada na ranar Juma'a da Lahadi kamar yadda suka saba duk da umarnin da gwamnati ta bayar na a rufe wuraren ibada a matsayin matakin dakile yaduwar kwayar cutar corona.

A cewar ministan, "gwamnatin tarayya tana sane da cewa wasu shugabannin addini da siyasa sun ki yin biyayya ga umarnin gwamnati na hana taron jama'a da yawa. "Akwai bukatar dukkan shugabanni su hada kai a lokaci irin wannan.

Dole su guji jefa rayuwar mabiyansu da sauran jama'a a cikin hatsari. "Akwai bukatar dukkan 'yan Najeriiya su kiyaye, su kuma kula da kansu, tare da daina zargin wasu da yi musu wata makarkashiya.

Ga wadanda suke ganin za su cigaba da karya dokokin da gwamnati kirkira domin dakile wannan annoba, nan bada dadewa ba dogon hannun hukuma zai kama su." Ministan ya bayyana cewa kwamitin da shugaba kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa a kan bullar annobar coronavirus zai fito da jerin wasu sabbin dokoki, kuma da zarar sun fito za a sanar da jama'a.

Kazalika, ya kara da cewa dukkan dokokin da za a kirkiresu ne domin kare 'yan Najeriya daga hatsarin annobar kwayar cutar corona da ke cigaba da mamaya a cikin kasa da duniya baki daya.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN