‘Yan kungiyar asiri sun kashe mai balangu sun arce da gasasshen nama a Abeokuta

Rahotun Jaridar Aminiya


A daren Juma’ar da ta gabata ne wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka dirar wa kasuwar Lafenwa a Abeokuta inda suka kashe wani mahauci mai suna Muhammad Tasi’u da ke sayar da balangu suka sassare shi, suka kwace masa kudi da wayar salula suka kwashi naman da yake sayarwa suka bar shi cikin jini lamarin da ya yi ajalinsa.

Sarkin Hausawa Abeokuta ya shaidawa Aminiya cewa, baya ga mahaucin ‘yan kungiyar asiri sun kashe karin mutum biyu a kasuwar ta Lafenwa inda suka jikkata wasu da dama, ” Sun zo shigewa ne cikin zuga domin suna da dimbin yawa cikin tsakiyar dare inda suka yi ta sare saren kan mai uwa da wabi, sun isa wajen mai sayar da nama, kamar za su saya sai suka haushi da duka da sara sun kwashe masa kudi da kayan cinikinsa da wayoyin salularsa suka tafi suka bar shi cikin jini.”

Sarkin Hausawan ya ce, an garzaya da mamacin asibiti inda aka ki karbarsa kafin daga bisani ya rasu, “Bayan mahaucin sun kashe wasu Yarbawa biyu a kasuwar.” in ji shi.

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, inda ya tabbatar da abkuwar lamarin, ya ce an kame shugaban kungiyar asirin, kana rundunar na ci gaba da farautar ragowar, ya ce zuwa yanzu zai iya tabbatar da mutuwar mutum daya ne, “Shi yasa jami’an mu a ko wani lokaci muke yaki da aikace-aikacen kungiyar asiri domin matsalar ba wai a tsakaninsu take tsayawa ba, tana shafar wadanda ba suji ba, basu gani ba.” in ji shi.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya 

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN