Yan daba sun kai wa Kwankwaso hari a Kano

Rahotun Legit Hausa
Wasu yan daba a Kano sun kai wa ayarin motocin tsohon gwamnan jahar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a ranar Talata, 17 ga watan Maris.
An tattaro cewa an lalata akalla motoci uku a ayarin nasa a lokacin faruwar lamarin wanda ya wakana a kusa da wani otel a birnin Kanon.
An rahoto cewa lamarin ya afku ne jim kadan bayan kwankwaso ya gana da Gwamna Fintiri.
A Wani jawabi daga Ibrahim Adam, kakakin Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna a zaben Kano na 2019, ya ce: “jigon ya tsere ba tare da rauni ba.”
Adam ya ce: “Yayinda ya ke barin otel din sai wasu yan daba da aka dauko haya suka farma ayarin motocin sanata Kwankwaso Sannan suka lalata motoci uku mallakar wasu yan majalisar dokokinmu.”
Ya Kara da cewa: “Amma Alhamdulillah, anyi taron cikin nasara. Basu cimma abunda suka so ba.”
A wani labari na daban, mun ji cewa Hukumar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta kashe yan bindiga da dama a ruwan wutan da tayi musu a Walawa, Yadi da tsaunin Kuduru dake jihar Kaduna.
A jawabin da diraktan yada labaran hukumar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya saki, ya bayyana cewa sun ragargaza sansaninsu da kayayyaki.
Hukumar Sojin saman sun kai wannan harin ne tare da hadin gwiwar hukumar yan sanda da wasu hukumomin tsaron Najerya.
Daramola yace an kai farmakin ne “bayan rahoton leken asiri ya bayyana yadda yan taaddan bayan korar mazauna daga muhallansu, suke cin karansu ba babbaka suna hallaka mutane.“
Yace “Hukumar NAF ta tura jirginta domin ruwan wuta sansanin yan bindiga inda aka lalata gidajensu tare da hallaka da dama cikinsu.“
“Harin jirgin saman ya baiwa sojojin kasa damar shiga cikin garuruwan domin karasa su.“
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN