Yadda dan shekara 26 ya yi wa mahaifiyarsa yar shekara 47 ciki, karanta dalili

Abin mamaki baya karewa a wannan Duniya ta Allah, domin a kullum mukan tashi ne da jin labarin ababe kala-kala. Wannan labarin wata mata ce mai suna  Mrs. Veronica Iorshe yar shekara 47 daga Mazabar Ugee ta dau cikin gaba da fatiha bayan dan cikinta da ta haifa ya yi ta aikata lalata da ita har tsawon wata biyu.

Wannan lamari ya faru a Aliade na karamar hukumar Gwer ta gabas a jihar Benue.

Maigidanta Sebastian Iorshe, dan shekara 44 ya aureta ne yan shekaru  da suka gabata, amma sai ya kasance Allah bai basu haihuwa ba. Amma kafin aurensu, dukanninsu sun taba yin aure, kuma maigidanta na yanzu ya rasa matarsa ta farko sakamakon rashin lafiya. Ita kuma ta rasa mijinta bayan wani hadarin mota, amma suna da 'da guda daya daga mijinta na farko.

Bayan tsawon lokaci da aurenta, kuma basu sami 'da ba da mijinta na biyu, sai yanuwan miji suka fara tsangwamarta, musamman mahaifiyar mijin, wacce ta ke zargin cewa tana amfani da dukiyar danta watau mijinta domin ta yi dawainiyar danta da ta zo da shi gidan.

Lamari fa ya yi zafi har mahaifiyar miji ta zo ta tare a gidan danta watau mijin matar,  sakamakon haka lamaurra suka kara jagulewa matar. Ganin haka ke da wuya, kuma tana matukar son mijinta, ta lallabe shi domin ya je ya yi gwajin maniyi amma sai ya ki.

Bayan tsananin matsin lamba a kan rashin haihuwa, sai matar ta lallabi dan cikinta da ta haifa da mijinta na farko watau Simon ya yi lalata da ita  har tsawon wata biyu. Sakamakon haka ta dau ciki.

Amma bayan ta shida wa mijinta cewa tana dauke da juna  biyu, sai ya ce alam baram shi fa wannan ciki ba nashi bane. Sakamakon haka suka dunguma zuwa wani Asibiti inda aka yi masu gwaji gaba daya wanda ya tabbatar cewa wannan ciki ba nashi bane domin kwayoyin maniyinsa basu da yawa da zasu iya yi wa mace ciki.

Daga karshe dai asiri ya tonu, kuma maigida ya koreta daga gidansa.

Daga Isyaku Garba, Muhammed Sani da Nura Kabiru.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN