Yadda Ali Kwara ya kwato bindigogi daga hannun ’yan ta’adda

Rahotun Jaridara Aminiya

Jaridar Aminiya ta labarta cewa fitaccen mai kama barayin nan Alhaji Ali Muhammad Kwara ya kwato miyagun makamai daga hannun ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane a gandun dajin Lame Burra da ke Jihar Bauchi.

Da yake mika makaman ga Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a Gidan Gwamnati, Alhaji Ali Kwara ya ce makaman an kwato su ne daga hannun wadansu miyagun mutane da ke da niyyar auka wa al’ummar jihar.

Da yake karbar bindigogin, Gwamna Bala Mohammed ya nanata kudirin gwamnatinsa  na tabbatar da tsaro ta hanyar hadin gwiwa da jam’ian tsaro da kuma Ali Kwara. Ya ce sun dade suna aiki da Ali Kwara da jami’an tsaro don magance matsalolin tsaro, sai ya yaba wa Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya saboda karfafa sanya masu ruwa-da-tsaki na  al’umma a harkar tsaro domin rage aikata laifuffuka,

Ya jinjina wa Alhaji Ali Kwara saboda namijin kokarin da yake yi sannan ya mika makaman ga Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi tare da yin alkawarin tallafa wa ’yan sandan da kayayyakin aikin da suka dace.

Da yake karbar makaman, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Mista Philip Mako ya nanata kudirin ’yan sanda na yin aiki tare da masu ruwa-da-tsaki domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar. Sai ya roki jama’a su shiga cikin shirin dan sanda da al’umma don kawar da miyagun mutane.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  

Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN