Tsige Sanusi II: Farfesa Auwal Yadudu da Sanata Shehu Sani sun yi magana

Rahotun Legit Hausa
A daidai lokacin da ake cigaba da magana game da siyasar Kano. Shehu Sani ya cewa wani abu game da matakin gwamnatin jihar na tunbuke Malam Muhammadu Sanusi II.
Shehu Sani ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV inda ya bayyana matsayarsa karara da cewa matakin da gwamnatin Kano ta dauka ya sabawa kundin tsarin mulki.
Sanata Sani ya bayyana cewa an tsige Muhammadu Sanusi II ne saboda ya na fadawa gwamnati gaskiya, a cewarsa gwamnoni jihohi ba su son su ji wani ya fito ya soke su.
A game da mukaman da gwamnatin Kaduna ta ba tsohon Sarkin, Shehu Sani ya ce Nasir El-Rufai ya yi hakan ne domin nuna goyon baya ga Abokinsa Muhammadu Sanusi II.
A cewar Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna a Majalisar baya, da wannan nadin mukamai, Mai girma El-Rufai ya aika sako ga wadanda su ka tsige Sanusi II daga kan mulki.
Shehu Sani ya na ganin akwai bukatar kawo dokokin da za su tsare rawanin Sarakuna
Sai dai duk da yadda gwamnatin Kaduna ta ke jan tsohon Sarkin Kano da aka tunbuke, Sani ya na ganin cewa shi kansa gwamna El-Rufai ba zai iya jurewa sukar jama’a ba.
Sani ya ke cewa da ace shi ma Sarki ne, da sun samu sabani da gwamnan na sa a cikin sa’a 24. ‘Dan siyasar ya yi kira ga masu mulki su daina jin haushin masu sukarsu.
Da ya ke magana, Sani ya ce gwamnatin Kano ta dade ta na taso Sanusi II a gaba, har ma ya ba sa shawarar cewa ya kalubalancin tsigesa da tsare sa da ake yi a gaban kotu.
Auwal Yadudu wanda fitaccen Masani ne a harkar shari’a ya goyi bayan Sanata Shehu Sani, ya nuna cewa babu shakka tsare Sanusi II ya ci karo da kundin tsarin mulki.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN