Sanusi II ya bayyana wadanda suka bada umarnin tsare shi


Rahotun Legit Hausa

Lamido Sanusi II ya ce an tube masa rawani ne ba tare da an bi ka’ida ba kuma hakan ba zai sa ya dauka mataki a kan gwamnatin jihar Kano ba, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Tsohon gwamnan bankin, wanda ya samu matsala da gwamna Umar Ganduje na jihar Kano tun 2017, an koresa daga jihar ne a ranar Litinin a sakamakon zarginsa da aka yi da rashin biyayya ga gwamnatin jihar. Gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Sarkin Kano na 14 ne bayan majalisar zartarwar jihar ta amince.


Ta kara da cewa Sanusi baya halartar tarukan da gwamnatin ta shirya ba tare da wani dalili ba wannan ta ce wannan adawa ce. Sanusi wanda yace an gagara bashi damar sauraro wanda hakan yasa aka tube masa rawani, ya ce umarnin kama shi, mayar da shi jihar Nasarawa daga Kano da kuma tsaresa da aka yi garin Awe na jihar Nasarawa, ya zo ne daga Abuja.

Ya yi ikirarin cewa Antoni janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami ne suka ba hukumar jami’an tsaro na farin kaya da ‘yan sanda tsare shi. Sanusi ya ce an hantaresa tare da gaggauta fitar dashi daga fadar ba tare da ya dauka kayan da suke mallakinsa ba.

Ya ce bayan sauke rawaninsa, wani abokinsa ya turo jirgin da zai kai shi Legas daga jihar Kano amma sai kwamishinan ‘yan sandar jihar yace a kai shi Abuja. Sanusi ya sanar da wannan ne a karar da ya shigar a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN