Tuddy Warebayigha, bayan ya harbi matarsa mai suna Charity da bindiga, sakamakon rikicin iyali dangane da yaya da suka haifa. Lamari da ya sa matar ta mutu.
Safeton dan sanda Tuddy Warebayigha, wanda ke aiki a caji ofis na yan sanda da ke garin Kaima a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma na jihar Bayelsa, ya bi matarsa ne zuwa hanyar gonarta, ya harbe ta a kafa, daga bisani ya harbe ta a ciki.
ISYAKU.COM ya samo cewa, safeton ya yi barazanar halaka duk wanda ya zo kusa da shi bayan ya harbi matarsa.
Rahotanni sun nuna cewa Safeto Tuddy dan barasa ne na gaske, kuma ya sha yin barazanar cewa zai koya wa matarsa hankali kamar yadda wani ganau ba jiyau ba ya fada wa Jaridar The Nation.
Kakakin hukumar yansandan jihar Bayelsa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama Safeto Tuddy, kuma yana fuskantar bincike a sashen CIID na rundunar.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari