Rikici ya balle tsakanin gwamnatin Kano, masarauta da kuma Nasiru Ado Bayero

Rahotun Legit Hausa
Sabon rikici ya kunno kai tsakanin gwamnatin Kano da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero a kan zargin ‘ka karba daga gareni kuma ka ci min dunduniya.’
Kamar yadda majiyoyi da dama suka gano, Dabo Fm ta ruwaito cewa Nasiru Ado bayero ya ki yarda da nadin da aka yi masa na sarkin Bichi bisa dalilai masu yawa.
Daga cikin dalilan kuwa akwai zargin cewa ya baiwa gwamnatin Kano da wasu masu nema masa Sarki harda uwargidan gwamnan Kano wasu kudade masu yawa, bayan anyi masa alkawarin za a bashi kujerar sarkin Kano ba ta Bichi ba.
Majiyar ta tabbatarwa da dabo Fm cewa Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero yayi ikirarin cewa yana da shaidun dukkanin kudaden da ya biya domin siyan sarautar gidan dabo.

A halin yanzu dai yana shaida cewa kodai a biya shi kudinsa da ya kashe ko kuma a mayar da Sarkin Kano Aminu Bayero Bichi shi kuwa ya komo sarautar Dabo.
Hakazalika, majiyar ta tabbatarwa da Dabo FM cewar akwai wasu shirye-shiryen da masarautar Kano takeyi na tube rawanin wasu hakimai da masu mukamai, ciki kuwa har da wazirin Kano.
Yanzu haka, majiyar ta kara da cewa akwai shirin dawo da waziri mai murabus, Sheikh Muhammad Nasir Muhammad kan mukaminsa na Wazirin Kano.
Biyo bayan tsige wasu daga cikin manyan kujeru da suka hada da Makaman Kano da sarkin dawaki mai tuta da sauransu, an gano cewa sun ci gaba da zuwa masarautar Kano din domin dama basu yarda da sabbin masarautun ba, kuma Muhammadu Sanusi II ya ci gaba da biyansu kudaden da ake basu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN