Mijina ya sakeni saboda kawai na tambaye shi ya bani izinin kwanciya da abokinsa

Rahotun Legit Hausa

Wata mata 'yar Najeriya mai suna Linda ta fada cikin tashin hankali bayan ta bukaci kwanciya da abokin mijinta don samun juna biyu. Linda tayi hakan ne kuwa don ta samu rabo bayan aurenta na shekaru takwas ya kasa samar da haihuwa.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, lamarin ya faru ne a Agodo Egbe da ke yankin Ikotun ta jihar Leagsa inda suke zama. Wannan bukatar kuwa ta jefa Linda cikin mummunan tashin hankalin da ya kai ga mutuwar aurenta, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa. Kamar yadda Linda ta bayyana:

 "A halin yanzu ina zaune da 'yan uwana ne a Ikorodu ta jihar Legas. Ina ta aikawa mijina ban hakuri da neman yafiya a kan bukatar da na mika gabansa. "Mijina Okey dan kasuwa ne babba don har kasashen duniya yake fita, yana shigo da kaya kala-kala. Yana da kadarori masu yawa a Legas da kuma Kudu maso gabas din Najeriya. Babban kalubalensa kuwa shine rashin haihuwa.

"Mun yi aure ne shekaru takwas da suka gabata amma har yanzu babu haihuwa. Mun je asibiti sannan fastoci da dama sunyi mana addu'ar samun rabo." Likitoci sun sanar da mijina cewa kwayoyin halittarsa basu da karfin kyankyashe kwai kuma yana ta karbar magani amma har yanzu shiru kake ji. Linda ta ci gaba:

"Na shiga damuwa saboda rashin sanin makomata a bangaren haihuwa. Mijina yace ya gaji da shan magunguna don haka ya mayar da hankali wajen kasuwancinsa. "Tun bayan da muka gane matsalarmu, na so karbar rikon yara amma ya hana ni.

Na ce ya samo mana mafita amma shiru. Sai na bashi shawarar ko zan kwanta da abokinsa yadda zan samu ciki mu haihu amma sai rigima ta barke. "Ya fara zargin cewa ina kwanciya da abokinsa ne shiyasa nake neman hanyar da zan halasta kwanciya da abokin shi. Daga nan ne kuwa ya fatattake ni tare da sakina."

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN