Mijin da ya ci amanar matarshi yaje yayi zina da wata a titi ya dauko cutar Coronavirus a jikinta

Rahotun Legit Hausa
Wani mutumi ya dauko cutar Coronavirus bayan yaje yayi lalata da budurwarsa a kasar Italy, yanzu haka dai an tsare shi tare da budurwar tashi a kasar Birtaniya, inda matar shi har yanzu bata san ainahin abinda yake faruwa ba.
Matar ba ta san yadda aka yi mijin nata ya kamu da cutar ba, amma mutumin ya bayyanawa ma'aikatan lafiya gaskiyar lamarin a kasar ta Ingila.
Mijin ya bayyana musu ya kamu da cutar ne a lokacin da ya tafi hutu da budurwar tashi a kasar ta Italy.
Wata majiya ta bayyana cewa: "Lamarin shi ya zama abin dariya. Mutumin ya bayyana ainahin abinda yayi a kasar Italy, kuma bai bayyanawa matarshi ba.
"Ya bayyana cewa ya dauki cutar a lokacin da ya tafi harkar kasuwancinsa. Duk da cewa ya bayyanawa ma'aikatan lafiya yadda lamarin ya faru, ya ce babu abinda za ayi masa ya bayyana sunan budurwar tashi.
Hakan na zuwa ne yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai kimanin mutane 1,543, inda mutane 56 kuma suka mutu sanadiyyar cutar a kasar ta Birtaniya.
Ana tunanin zai samu lafiya, amma kuma hankalinshi yayi matukar tashi saboda yana tsoron kada matarshi ta san da zancen.
Amma majiyar ta ce Allah ne ya taimakeshi ya dawo kafin a dakatar da sauran kasashen duniya zirga-zirga saboda cutar.
Mutumin ya fito daga kasar ta Italy kafin a dakatar da zirga-zirga a kasar, wacce tafi kowacce kasa a yankin Turai yawan masu dauke da cutar, inda sama da mutane 2,158 suka mutu.
Mutuminda yafi tsufa a cikin wadanda suka mutu din a kasar shine, wani mai shekaru 95, wanda kuma yafi kankanta sune wasu mutane biyu da suka mutu masu shekaru 39.
A yanzu dai a yankin Lombardy, inda cutar tafi kamari a kwanakin baya an fara samun saukin lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN