Rahotanni da Jaridar Daily Trust ta wallafa sun nuna cewa jami'an tsaro da aka girke a kofar shiga sakatariyar jam'iyar APC ta kasa a Abuja sun hana wasu masu taimaka wa Adam Oshiomhole wajen aiki shiga Sakatariyar.
Ma'aikatan sun je Sakatariyar ne a cikin wata mota kirar Toyota Jeep mai launin baki, amma sai jami'an tsaron suka hana su shiga, duk da yake sun nuna shaidar cewa su masu taimaka wa Oshiomhole ne a wajen aiki.
Daily Trust ta ce jami'an tsaron sun bukaci mutanen su jaye motarsu daga kofar shiga Sakatyariyar, yayin da sauran masu sa ido kan lamurra ke kallo a gefe daya.
Jaridar ta kara da cewa kimanin motoci 20 ne dankare da jami'an tsaro ke sintiri a titin Blantire da ke Wuse 2, inda Sakatariyar APC ke da mazauni a birnin tarayyar Najeriya Abuja.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari