Rahotun Legit Hausa
Gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammad ya yi umurni kamawa da hukunta tsoffin gwamnoni Isa Yuguda da MA Abubakar wadanda ake zargi da sace kadarorin gwamnatin jahar na triliyoyin nairori a lokacin da suke kujerar mulki.
Gwamnan ya bayar da umurnin ne lokacin da ya samu rahoton kwamitin kwato kadarorin jahar da aka nada a ranar 12 ga watan Yuli, 2019 sannan aka umurce su da su binciki zargin karkatar da kadarori a tsakanin 2007 da 2019 a zauren majalisa, gidan gwamnatin Bauchi.
Gwamna Bala wanda ya ce lallai dole jami’an gwamnati su kasance da bayanan abubuwa dalla-dalla ya sha alwashin dawo da arzikin jahar da kuma tabbatar da hukunta tsoffin gwmnonin da jami’ansu da kwamitin ya samu da laifi.
Ya ce atoni janar na jahar da wasu mambobin kwamitin Za su hadu su yi nazari a kan shawarwarin da kwamitin dawo da dukiyoyin suka bayar don hukunta wadanda ke da hannu a ciki.
Mukaddashin shugaban kwamitin, Ritaya Janar Markus Koko Yake yayinda yake gabatar da rahoton ga gwamnan ya ce kwamitin ta gano badakala daban daban da kuma karkatar da kadarorin gwamnati daga ma’aikatu, da hukumomi 19 takanin 2007 da 2019 lokacin da Yuguda da Mista Abubakar suka yi shugabanci a matsayin gwamnonin jahar.
An tattaro cewa kwamitin ya bukaci tsoffin gwamnonin da sauransu da su dawo da kudaden da ake zargin sun sata a lokacin mulkinsu.
DAGA ISYAKU.COMLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Tags:
LABARI