Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi

Rahotun Legit Hausa
Fadar shugaban kasa tayi martani a kan zargin kaiwa shugaban kasa Muhammad Buhari hari da aka yi a jihar Kebbi a ranar Alhamis.
Wani bidiyo dai ya bayyana inda wani matashi ke ta kokarin cafko shugaban kasa Muhammadu Buhari a bikin baje kolin kamun kifi da aka yi a jihar Kebbi. Wannan bidiyon kuwa ya jawo cece-kuce daga wajen ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani.
A wata takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, ya ce matashin dai masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba harar shi yayi niyya ba.
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kebbi a ranar Alhamis don bude taron bikin baje kolin kamun kifi da al'adun gargajiya na jihar Kebbi.
"Wannan ne karon farko da za a yi bikin wanda ke jawo hankulan jama'a daga kasashe daban-daban a shekaru 11 da suka gabata. An daina bikin ne tun bayan tsanantar rashin tsaro.
"A yayin da shugaban kasar ke rangadi a wajen don duba shinkafar da manoma suka kawo tare da daukar hoto dasu, sai wani matashi da farin ciki ya cika ya kusanto shugaban kasar. Yayi kokarin kaiwa garesa."
Ya kara da cewa, "Sanannen abu ne cewa hakan ba za ta yuwu ba. Jami'an tsaro kuwa sun hana matashi kaiwa gareshi wanda yasa matashin ya dinga kara yunkuri. A halin yanzu manyan 'yan adawa na cewa harar shugaban kasar yayi niyya. Makiya sun saba juya abun alheri zuwa sharri. Amma kansu suke ba haushi don kullum kasar na samu ci gaba,"
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN