Coronavirus ba sabon abu ba ne - Sheikh Aminu Daurawa

Rahotun Legit Hausa
Shahararren malamin nan na addinin Musulunci kuma tsohon Shugaban hukumar Hisbah ta jahar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya yi martani a kan barkewar cutar coronavirus a fadin duniya.
Daurawa ya bayyana cewa an jima ana haduwa da ibtila’i a fadin duniya kama daga annobar zawo da amai da sauran cututtuka da ke yaduwa sannan suka dade suna addabar duniya, sannan cewa ana yi masu fassara daban-daban, shafin BBC Hausa ta ruwaito.
A cewar shehin malamin, ta fuskacin addini aana daukar annobar ne a matsayin jarrabawa da jan kunne da Allah ke yi wa al’umma don su saduda su koma ga Allah, su yadda cewa akwai mai duniya, sannan kuma yana da ikon tayar da ita a duk lokacin da ya so hakan.
Ya ce: "An dade ana hasuwa da jarabta a fadin duniya, kama daga cutar kwalara da Annoba da yaduwar cutaka wanda ya dade yana addabar duniya, kuma ana yi masa fassara iri- iri, kowa gwargwadon abin da yake dauke da shi na akida ko hankali ko ilmi ko al'ada ko surkulle.
"Amma mu ta bangaren addini muna daukar hakan a matsayin ibtila'i da jan kunne da Allah yake yi wa mutane domin su saduda, su sallamawa Allah, su yadda wannan duniya akwai me ita, kuma yana da iko akanta kuma zai Iya tashin ta duk sadda yaga dama...
"Mu yi abubuwa biyar:
"Na daya shine yarda da kaddara mai dadi ko mara dadi duk daga Allah ne
"Mu dauki matakan kare kanmu kamar yadda jami'an kiwan lafiya suke fadi
"Mu koma ga Allah da istigfari saboda ya yaye mana wananan Annobar, da yawaita zikri da addua.
"Duk musulmin da ya rasa ransa yayi shahada.
"Kada mu shiga inda Annoba take, kada kuma mu fita daga inda ake yi har sai an tabbatar da bamu dauka ba."
A wani labari na daban, mun ji cewa Ofishin hukunta jama’a a kasar Saudiya a ranar Alhamis, 20 ga watan Maris, ya bayar da umurnin kama wasu mutane biyu da suka bayyana a wani bidiyo inda suke dirki maganin kashe kwayoyin cuta don tsoron kamuwa da Coronavirus.
An gano matasan a lokuta mabanbanta suna dirkar maganin kashe kwayoyin cutar a wani bidiyo da ya shahara, inda hakan ya haifar da zafafan sharhi a yanar gizo.
A safin Twitter, ofishin hukunta jama’ar ta yi umurnin kama mazajen kan shan sinadaren kashe kwayoyin cutar wanda bai dace da garkuwar jikin dan Adam ba da kuma batar da jama’a cewa hakan zai kare su daga cutar coronavirus.
Kasar Saudiyya ta samu mutane 274 da ke dauke da coronavirus amma babu wanda ya mutu zuwa yanzu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN