Zargi: Bagudu, Ekweremadu, Etete, da mutane 334 su na da kadarorin N152b a Dubai

Rahotun Legit Hausa

Gwamna Atiku Bagudu da Sanata Ike Ekweremadu su na cikin wadanda aka ambaci sunayensu a jerin ‘Yan siyasar Najeriyar da su ke dankare da gidaje da kadarori a boye a kasar UAE.

A wani bincike da wani Mutumin kasar waje mai suna Mathew Page, ya yi a kan shugabannin Najeriya, ya gano cewa akalla ‘Yan kasar 331 da su ka tara dukiya a kasar Larabawan. Mista Mathew Page ya bayyana cewa wadannan Bayin Allah sun mallaki dukiyar Dala miliyan 400 watau N152b a UAE. Daga cikin wadanda aka ambata akwai Jiga-jigan PDP da APC.

Wata Jarida ta bayyana cewa daga cikin wadanda lambarsu ta fito akwai Sanata Atiku Abubakar Bagudu wanda yanzu haka shi ne gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban gwamnonin APC. Atiku Bagudu ya na da gidaje akalla takwas a Dubai wanda kudinsu ya kai Dala miliyan 4.8.

Haka shi ma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ba a bar shi a ba yab Ike Ekweremadu ya na da gidaje da aka yi lissafin kudinsu a Dala miliyan 7, Sanatan ya mallaki gidajen ne a wani wurin shakatawa da kuma Burj Dubai. Bayan haka ya na da gidaje a Ingila.


Ana zargin cewa Sanata Ike Ekweremadu ya na da gidaje a Birtaniya da UAE Source: Depositphotos Binciken ya nuna cewa akwai tsofaffin Gwamnoni da Sanatoci, da kuma Kwamishinoni, da shugabannin hukumomin gwamnati da ‘yan canji da su ka mallaki kadarori a kasar ta UAE. Sauran manyan Najeriya da ake zarginsu da dukiyoyi a Dubai sun hada da tsohon shugaban PDP, Ahmadu Ali, tsohon gwamnan Kwara, Mohammed Lawal da tsohon Minista Dan Etete. Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ibrahim Mantu ya na cikin wadanda aka ambaci sunansu.

Haka zalika tsoshuwar shugabar bankin nan na Oceanic, Cecilia Ibru. Har ila yau a wannan jeri akwai Tafa Balogun wanda ya rike IGP a Najeriya, da kuma Bala Mshelia, da tsohon shugaban NNPC Ladan Shehu da Takwaransa na PPMC, Samuel Okeke. Rahoton binciken ya ambaci tsohon gwamnan Delta, James Ibori wanda aka taba daurewa a kurkuku.

A takaice dai mutane 156 sun mallaki gidaje da kadarori 226 a Garin na Dubai. Wannan rahoto ya ambaci gwamnoni 35, ‘Yan majalisa 45 da shugabannin ma’aikatu 14. Akwai kuma sunayen tsofaffin Ministoci 15 da Ma’aikatan NNPC da fadar shugaban kasa da Alkalai.

Rahotun Legit Hausa




DAGA ISYAKU.COM




Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN