An dakatar da dan majalisar jihar Jigawa saboda 'kai wa tawagar gwamna hari'

Rahotun Legit Hausa

Majalisar jihar Jigawa a ranar Juma'a ta dakatar da mamba mai wakiltan mazabar Gumel, Sani Isiyaku dan jami'iyyar APC a kan zarginsa da amfani da 'yan daba.

Ana zarginsa ne da hada baki da wasu 'yan daba da suka kai wa tawagar gwamnan jihar hari. Premium Times ta yi kokarin ji ta bakin dan majalisar ta wayar tarho amma hakan bai yi wu ba domin lambarsa ba ta shiga a lokacin hada rahoton.

Kakakin majalisar jihar, Idris Garba ne ya sanar da dakatar da shi a zaman majalisar na ranar Alhamis. Ya ce dukkan 'yan majalisar sun amince da matakin dakatar da shi.

Kakakin majalisar ya ce dan majalisar da aka dakatar ya hada baki da wasu 'yan siyada da 'yan bangan siyasa domin inda suka 'dauke hankalin' tawagar gwamna Muhammad Badaru yayin da suke karamar hukumar Hadejia

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post