An dage auren matashi dan Kano da masoyiyarsa baturiyar Amurka

Rahotun Jaridar Aminiya

An dage daurin auren matashin nan dan jihar Kano Isa Sulaiman da masoyiyarsa baturiyar Amurka Jeanine Sanchez wanda a baya aka shirya yi a watan da muke ciki bayan da ta ziyarce shi a gidansu da ke Fanshekara a watan Janairun da ya gabata.

Mahaifin matashin Malam Sulaiman Isa ne ya shaidawa Aminiya hakan, ta wayar salula inda ya ce an dage daurin aure, ba a kuma sake sanya rana ba sai zuwa lokacin da baturiyar zata samar masa

takardun izinin zama ƙasar Amurka, ya ce dage daurin auren ya biyo bayan matakin hana wa ‘yan Najeriya biza da kasar Amurka ta dauka.

Sulaiman, mai shekaru 25 wanda ke karatu a jami’ar Bayero ta Kano ya shirya auren masoyiyarsa baturiyar Amurka mai ‘ya’ya biyu bayan sun hadu da ita a kafar sada zumunta ta instagram kimanin shekara guda da ta shude inda ya yi niyyar ci gaba da karatunsa a Amurka bayan an daura auren nasu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN