An bayyana shirin tsohon sarki Sanusi II na gaba bayan tube rawaninsa

Rahotun Legit Hausa

Sananne a kafar yada labarai, Dele Momodu a ranar Litinin ya kai wa tubabben sarkin Kano, Sanusi Lamido ziyara a Legas. Sanusi, wanda ya samu 'yancinsa bayan wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin gaggawar sakinsa, a halin yanzu yana jihar Legas.

A yayin ziyarar da Momodu ta kai wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya din, ya ce sam wannan hukuncin na gwamnatin jihar Kano bai bata wa basaraken rai ba. Sananne a kafar yada labarai ya bayyana cewa, a halin yanzu Sanusi na kokarin ganin yadda zai amfani al'umma ne da gogewarsa. Idan zamu tuna, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a cikin sa'o'i 48 bayan tubewa tsohon sarkin Kano din rawani, ya bashi mukamai har biyu a jihar.

A shafinsa na twitter, Momodu ya rubuta: "Na dau lokaci mai inganci da amfani a tare da tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da wannan yammacin. Yana cike da burin ci gaba kuma bai nuna damuwarsa ba a kan abinda ya faru. "Ya zabi ci gaba da ayyukan da zasu amfani al'umma da gogewarsa hadi da iliminsa. Ina masa fatan alheri."

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN