• Labaran yau


  2023: Kungiya ta shirya tsaf domin mara wa Abubakar Malami a Birnin kebbi

  Wata kungiya mai karadin ganin Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami SAN ya fito takaran Gwamnan jihar Kebbi mai suna Khadi Malami Progressive Association, ta gudanar da tatattaunawa a garin Birnin kebbi.

  Yan kungiyar sun hadu a kofar gidan Sarkin Fawa da ke unguwar tsohuwar kasuwa ranar Asabar 21/3/2020 inda suka tattauna kan alfahari da yiwuwar fitowar dan unguwar Junju, domin takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a 2023.

  Haka zalika, yan kungiyar, sun tattauna yadda za su shiga Birni da kauyuka domin nemo jama'a su mara wa tafiyar.

  Daga karshe, 'yan kungiyar sun sha alwashin cewa za su shiga yin kamfen, domin wannan tafiya idan lokaci ya yi, kuma a yanzu, sun dukufa ne domin bayyana ayyukan alkhairi da Abubakar Malami yake yi wa jama'a.

  Zaman ya sami jagorancin shugaban kungiyar Dan Yaya Milo, tare da Sakataren kungiyar Ahmed Didiyu. Sai kuma Dattijan kungiyar Mal.Habibu B, Bashir Magini da Mansur S. Fawa.

  Kungiyar na da tsari gida uku da suka hada da manyan matasa, kananan matasa da kuma mata.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 2023: Kungiya ta shirya tsaf domin mara wa Abubakar Malami a Birnin kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama