Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatar da Modibbo-Kawu a matsayin shugaban NBC

Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Ishaq Moddibo-Kawu a matsayin Direkta Janar na Hukumar Watsa Labarai ta kasa NBC kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito a ranar Juma'a. Majiyar Legit.ng ta gano cewa an dakatar da shi ne bisa shawarar da Hukumar Yaki da Masu Aikata Rashawa, ICPC, ta bayar ta ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Majiyar ta ce wasikar ta yi umurnin babban direktan a hukumar ya maye gurbin Moddibo-Kawu kafin a kammala binciken da ake gudanar wa a kansa. "Don haka, Armstrong Idachaba, direktan sashin kula da watsa labarai zai kama aiki a matsayin shugaba na rikon kwarya," in ji majiyar. Wani ma'aikacin NBC da ba a bawa izinin yin magana da kafafen watsa labarai ta shaidawa majiyar Legit.ng ya ce tuni Moddibo-Kawu ya kwashe kayayyakinsa daga ofishinsa. Idan ba a manta ba dai ana ICPC na bincike a kan zargin damfara ta Naira biliyan 2.5 da aka ce an biya Pinnacle Communications Ltd a matsayin kudin da za su fara aikin sauya tsarin watsa labarai zuwa na zamani wato Digital. An gano cewa tun a watan Satumban 2019 ne hukumar ta ICPC ta bayar da shawarar a dakatar da Modibbo-Kawu a cikin wasikar da ta aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha Read more: https://hausa.legit.ng/1302657-yanzu-yanzu-buhari-ya-dakatar-da-modibbo-kawu-a-matsayin-shugaban-nbc.html
Rahotun Legit Hausa

Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Ishaq Moddibo-Kawu a matsayin Direkta Janar na Hukumar Watsa Labarai ta kasa NBC kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito a ranar Juma'a. Majiyar Legit.ng ta gano cewa an dakatar da shi ne bisa shawarar da Hukumar Yaki da Masu Aikata Rashawa, ICPC, ta bayar ta ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Majiyar ta ce wasikar ta yi umurnin babban direktan a hukumar ya maye gurbin Moddibo-Kawu kafin a kammala binciken da ake gudanar wa a kansa. "Don haka, Armstrong Idachaba, direktan sashin kula da watsa labarai zai kama aiki a matsayin shugaba na rikon kwarya," in ji majiyar.

Wani ma'aikacin NBC da ba a bawa izinin yin magana da kafafen watsa labarai ta shaidawa majiyar Legit.ng ya ce tuni Moddibo-Kawu ya kwashe kayayyakinsa daga ofishinsa. Idan ba a manta ba dai ana ICPC na bincike a kan zargin damfara ta Naira biliyan 2.5 da aka ce an biya Pinnacle Communications Ltd a matsayin kudin da za su fara aikin sauya tsarin watsa labarai zuwa na zamani wato Digital.

An gano cewa tun a watan Satumban 2019 ne hukumar ta ICPC ta bayar da shawarar a dakatar da Modibbo-Kawu a cikin wasikar da ta aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari