Akalla mutum biyu sun mutu, fiye da goma sun bace sakamakon wani mumunar rikici da ya barke a garin Isu na karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia ranar Litinin, sakamakon jayayya kan iyaka da makwabatansu na al'umman Biase da ke karamar hukumar Ukwa Odokpani a jihar Cross Rivers.
ISYAKU.COM ya samo cewa al'umman garin Isu sun sha fama da mumunar tashin hankali da ke salwantar da rayuka sakamakon rikicin iyaka da makwabatansu na garin Utama a jihar Cross Rivers, tun shekaru da dama da suka gabata.
Rahotanni sun nuna cewa wasu yan bindiga dadi ne suka kai hari da misalin karfe 8 na dare suka buda wuta da bindigogi a garin Isu, daga bisani suka gudu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari