Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai


Rahotu Legit Hausa

Wani mutum a kasar Brazil ya amsa cewa ya kashe matarsa ne a yayin da suke tsakiyar saduwa saboda fushin cewa ta sake samun juna biyu karo na uku.

Marcelo Araujo dan shekara 21 ya shaidawa 'yan sanda a Sao Paulo bayan an shafe makonni shida ana masa tambayoyi cewa ya kashe matarsa mai sana'ar yi wa mutane kwaliya, Francine dos Santos, mai shekaru 22 bayan sunyi musayar kalamai kan juna biyun da ta sake dauka karo na uku.

Ya bayyana cewa baya son karin haihuwa saboda ya ki jinin yadda hankalin matar ke rabuwa tsakaninsa da yaran kuma yana matukar damuwa saboda kudin da ya ke kashewa domin kulawa da yaran. Ma'uaratan suna da yara biyu, mace mai shekaru hudu da na miji dan shekara biyu.

Da ya ke bayar da ba'asi kan yadda rikicinsu ya samo asali, Mista Araujo ya yi ikirarin cewa a watan Decemban 2019, sun fara tattauna yadda za su yi bikin Kirsimeti amma sai suka fara musayar kalamai a kan juna biyun da ta ke dauke da shi.

Jim kadan bayan sun kammala musayar kalaman, sun huce fushinsu kuma suka nufi daki domin suyi kwanciya irin ta masoya. A yayin da suke tsakiyar saduwa ne wanda ake zargin ya yi amfani da wuka ya yi ta caka wa matarsa kuma daga bisani ya yanke ta a wuya.

Bayan ya aikata laifin, ya yi yunkurin ya kashe kansa. Yan sanda sun tsinci shi da munanan rauni a wuyansa da hannunsa a gidansu da ke Varzea Paulista da ke jihar Sao Paulo.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN