Mutane 10 da suka fi kowa arziki a Najeriya a 2020 da kiyasin dukiyarsu (Hotuna)

Rahotun Legit Hausa
Akwai manyan masu arziki a nahiyar Afirka da a kowacce shekara suke shiga jerin masu kudin duniya a mujallar Forbes da sauran mujallu. Najeriya kasa ce mai cike da jama’a masu tarin dukiya. Kasuwanci ne jigon arzikin mafi yawan su.
Duk da cewa kuwa, kungiyoyi da dama kan yi sharhi ko kuma bayyana mutane masu arziki, toh ba kowanne mai arzikin ake hadawa dashi ba. A kowanne shekara kuwa a kan samu sauyi a jerin masu kudin. Hakan na nuna cewa wasu na samu ne inda wasu ke tafka asara ko kuma su rasa saboda wasu dalilai. Ga jerin manyan masu kudin Najeriya da adadin dukiyarsu a 2020.
10. Fifi Ekanem Ejindu - $850 million
Fifi Ekanem mace ce mai kamar maza. An san ta ne da kamfaninta mai suna neo-traditional kuma hakan yasa ta samu lambobin yabo saboda hazakarta. Ba a nan Fifi ta tsaya ba, tana kasuwancin man fetur da iskar gas tare da dillanci.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
9. Hajia Bola Shagaya - $950 million
Najeriya na da mata masu kamar maza wajen jajircewa a neman arziki. Hajia Bola Shagaya ta shiga jikin manyan bankin Unity na shekaru da dama. Kasuwancinta sun shafi kyale-kyale ne da sauransu.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
8. Jim James Ovia - $980 million
Waye bai san bankin Zenith ba? Bankin na daya daga cikin manyan masana’antun kudi a Najeriya kuma Jim Ovia ne ya kirkiro shi. A matsayin shi na daya daga ciki manyan masu kudin da ya mallaki makuden kudade.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
7. Orji Uzor Kalu - $1 billion
Hamshakin mai dukiya ne amma kudinsa sun dan ragu saboda faduwar kudin gidaje da kuma man fetur.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
6. Folorunsho Alakija - $1 billion
Folorunsha Alakija ta kasance mace mai kamar maza. Kasuwancinta ya shafi man fetur da kyale-kyale. Ta bayyana a mace baka mafi arziki a duniya kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa. Ta fi kowacce mace kudi a Najeriya.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
5. Pascal Uzoma Dozie - $1.1 billion
Wannan dan kasuwar na daya daga cikin ‘yan kasuwa da suke da hannayen jari a bankin Diamond, Kunoch Limited da sauransu. Shine shugaban MTN a Najeriya.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
4. Jimoh Ibrahim - $1.1 billion
Jimoh Ibrahim ya samu nasarar arzikinsa ne ta hanyar sana’ar man fetur. Shi ne mamallakin Global Fleet Group. Kasuwancinsa sun hada da inshora, otal, dillanci da sauransu.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
3. Femi Otedola – 1.8 billion
Femi Otedola ne mai babban hannun jarin da ke juya kamfanin mai na Forte Oil. Arzikinsa ya matukar shahara.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
2. Mike Adenuga - $7.2 billion
Mike sananne ba a Najeriya kadai ba, har da duniya sakamakon kamfaninsa na Globacom. Kasuwancinsa sun yawaita ne har a Afirka ta yamma.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
1. Aliko Dangote - $9.9 billion
Wannan suna ba sai anyi bayani a kan shi ba. Babban dan kasuwa ne wanda ya saka hannayen jari a kasuwanci kala-kala. Shi ne bakin mutum mafi arziki a duniya baki daya.
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN