Likitocin ‘Ya ‘yan mutum daya da kowa ya ke ta magana a kansu

Rahotun Legit Hausa
Wata Baiwar Allah ta wallafa hotunan Mata biyar wanda ta bayyana cewa ‘Yanuwan juna ne, da su ka yi tarayya a wajen aiki.
Duka wadannan Mata da su ka dauki hoto, Likitoci ne kamar yadda za a fahimta daga yanayin kayan da su ke dauke da shi.
A kasashe irin Najeriya, an saba ganin Likitoci a matsayin Maza, inda ake barin Mata da irinsu aikin Ungon-zoma da sauransu.
Yanzu abubuwa sun fara canzawa, wadannan Mata cikin kayan asibiti da hotonsu ya ke yawo, duk sun fito ne daga gida daya.
Kamar yadda mu ka samu labari daga wajen wanda ta wallafa hoton; daga cikin Matan akwai kwararriyar Likitar kwakwalwa.

Daya kuma Likitar aikin mata ce, yayin da guda kuma ta zama Likitan Iyali. Daya daga cikinsu kuma Likitar al’umma ce.
Ta karshen su kuwa ta kware ne a fannin yin aikin fida na canza yanayin jikin mutane. Dukansu mutum daya ya haife su.
A Najeriya dai ana fama da karancin Likitocin kwakwalwa da kuma Likitocin da ke fidar da ke canza kamannin mutane.
Atiku Abubakar ya yi magana game da wadannan mata, inda ya ce duk wanda ya ba Mace ilmi, ya ilmantar da al'umma
Dazu kun ji labari cewa tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, ya kan yi kuka idan ‘Ya ‘yansa su ka samu wata daukaka.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN