Kungiyar Arewa ta sake taso Buhari a gaba, ta nemi ya yi murabus gaba daya


Rahotun Legit Hausa

Taron kungiyoyin Arewa a karkashin lemar NYSC sun fadawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a dalilin rashin tsaro da ake ta fama da shi yayin da ya ke ofis. NYC ta koka game da kashe-kashen da ake yi a halin yanzu a Najeriya, wannan ya sa kungiyar ta ce lokaci ya yi da shugaba Buhari zai tattara kayansa ya bar kujerar mulki.

A cewar kungiyar NYC ta bakin shugabanta na kasa, Muhammad Ishaq, zai fi dacewa da Muhammadu Buhari ya yi murabus kafin Najeriya ta zama irin Somaliya. Mista Muhammad Ishaq ya yi wannan jawabi ne a birnin tarayya Abuja, ya na mai cewa kasar ta koma halin da ta shiga ciki a lokacin da Goodluck Jonathan ya ke mulki.

Da ya ke magana a Ranar Laraba, Ishaq ya bayyana cewa sha’anin tsaro ya tabarbare, kuma a kan hakan ne ma aka yi waje da gwamnatin baya ta jam’iyyar PDP da ta shude. Kungiyar ta nuna cewa shugaban kasa Buhari ya gaza cika alkawarin da ya yi wa 'Yan Najeriya na cewa zai kawo zaman lafiya a fadin kasar idan har aka zabe shi.

Ko dai ace halin da ake ciki ya fi na lokacin Jonathan tabarbarewa ko kuma ace akalla abin ya kai irin abin da ya auku a lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan. Ganin kura ta kai bango a halin yanzu, Mista Ishaq ya ce: Lokaci ya yi da ba za a iya cigaba da daukar wani uzuri ba.

“Buhari ya gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma. NYC ta kare jawabin ta da cewa: “Watakila bai da niyyar yin haka ne, ko kuma ba zai iyan ba, don haka ya yi murabus, ya ceci kasar nan daga wargajewa gaba daya.” 


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN