Alkalin baban Kotun tarayya da ke birnin Sokoto Jastis Bello Duwale, ya yanke wa wani dan damfara mai suna Bashar Umar Abdullahi (a.k.a Abdu Abdullahi and
Bashir Abdullahi) daurin shekara daya a Kurkuku babu tara.
Kotu ta kama Bashar da laifin damfaran wani mai suna Abubakar Umar Lugga yayin da ya bukaci Bashar ya taimaka masa domin ya zari kudi ranar 29 ga watan Maris 2019, amma sai Bashar ya yi amfani da katin ATM na Abubakar, wanda na First Bank ne, ya tura kudi Naira dubu goma sha biyar (N15,000.00) zuwa asusun wani Aminu Ahmed a Eco Bank mai lambar ajiya 3050002223.
Hukumar EFCC reshen Sokoto, ta gurfanar da Bashar a gaban Kotu bisa tuhumar damfara, a karkashin doka mai lamba 320 na Penal Code, kuma zai fuskanci hukunci a sashe na 322 na dokar ta Penal Code.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari