Ranar Juma'a 28 ga watan Fabrairu an sami rahotun matsala ta farko kan cutar a birnin Lagos.
Ministan Lafiya Osagie Ehanirem, ya fitar da wani tsari da mutum zai iya kare kansa da yardar Allah.
1. Ka wanke hannayen ka da sabulu a koda yaushe, watau lokaci-zuwa lokaci
2. Ka kasance akalla mita daya (1) ko kafa biyar (5 feets) daga duk wanda ka gan yana tari ko atishwa.
3. Wadanda suke atishwa, fama da mura, sai su zauna a gida domin kada su yi cudani da jama'a kafin su sami sauki.
4. Idan kana fama da tari ko atishawa, kada ka kwana daki daya tare da wadanda basu tari ko atishawa, kuma ya kamata ya kasance akwai isasheshen iska. Ka rufe bakinka da kyalle ko abin kare shakar iska idan kana fama da mura ko tari.
5. Ka kira wannan lamba domin karin bayani kan lamarin cutar Corona Virus, ko idan kana zargin cewa wani, ko kai ka kamu da cutar, sai ka kira NCDC a wannan lamba 0800-970000-10. domin karin bayani
6. Ka dinga sauraron labarai a Rediyo ko Talabijin, dasauran kafafen labari, domin sanin yanayi da ake ciki dangane da cutar COVID-19 (Korona)
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari