Gwamnatin Buhari ta shiga yarjejeniya da kasar Amurka game da dawo da kudaden Abacha gida

Rahotun Legit Hausa

Gwamnatin Najeriya, gwamnatin kasar Jersey da gwamnatin kasar Amurka sun rattafa hannu kan yarjejeniyar dawo da kudaden da tsohon shugaban Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha ya jibgesu a kasashen waje.

Punch ta ruwaito ofisoshin jakadancin Najeriya da na Amurka ne suka bayyana haka a ranar Litinin, inda suka ce yarjejeniyar ta amince da dawo ma gwamnatin Najeriya kimanin dala miliyan 308 mallakin Abacha.

An tura wadannan kudade ne ta bankunan kasar Amurka, inda aka jibgesu a asusun bankin kasar Jersey da sunan wani kamfani Doraville Properties Corporation, wanda yaron Abacha ke shugabanta. A shekarar 2014 ne wata kotun Amurka ta bayyana kudin a matsayin haramtattu da aka sace a tsakanin shekarun 1993 da 1998, daga nan babban lauyan Jersey ya nemi daman daskarar da asusun bankin Doraville, kuma kotu ta sahhale masa.

Ana zargin Abacha da abokansa na kusa dun wawure makudan kudade daga lalitar gwamnati a miliyoyin daloli a zamanin mulkinsa wanda hakan ya kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar, daga cikin wadanda suka kwashe kudaden akwai yaransa Ibrahim da Muhammad, da wasu yan uwansa na kusa.

Wasu daga cikin kasashen da aka kwato kudaden Abacha sun hada da Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus, Switzerland, Lichtenstein da kuma Luxembourg, a shekarar 2018 aka fara sabon tsare tsaren maido da kudaden Najeriya, sai a cikin makonnan aka kawo karshen tsare tsaren da rattafa hannu. Yarjejeniyar da aka kulla ta tanadi a kashe kudaden wajen yi ma yan Najeriya aiki, kuma gwamnatin Najeriya za ta kafa kwamitin sa ido don tabbatar gaskiyar yadda aka kashe kudaden.

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai shirin daukan sabbin zaratan Sojoji nan bada jimawa ba a kokarin gwamnatin Najeriya na kara adadin jami’an tsaro domin su kawar da matsalar tsaro a kasar. Osinbajo ya bayyana cewa: “Muna yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen matsalar tsaro, muna tafiyar da tsaron nan yadda ya kamata, daga ciki har da aika Sojoji bakin daga domin yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

“Har ma a yanzu zamu kara daukan sabbin Sojoji a rundunar Sojan kasa, kuma zamu dauke su ne a tsarin gaggawa, kuma zamu sayi karin makamai da sauran kayan aiki. A zaman karshe da muka yi na majalisar tsaro mun tattauna yiwuwar kara yawan Sojoji“Mun tattauna yadda zamu hada kai da matasa jarumai yan sa kai da sauran yan banga, don haka muna aiki tukuru wajen tsaurara matakan tsaro, musamman yadda zamu yi amfani da na’ura wajen leken asiri a kasar.” Inji shi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN