Duba amfanin citta guda 4 a jikin dan Adam na 3 zai baka mamaki

Rahotun Legit Hausa
A garinta, danya ko busasshiya, citta na da amfani kuma tana taka rawa wajen inganta lafiyar dan Adam. Ga kadan daga cikin amfanin citta kamar yadda masana kiwon lafiya suka tabbatar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
1. Citta na maganin tasowar amai
Tasowar amai na daga cikin alamu na zazzabi ko kuma juna biyu. Alama ce ta wasu ciwuka kuma kwata-kwata yana hana mutum sakewa. An gano cewa citta na maganin tasowar amai ko wanne iri ne kuwa.An gano cewa citta na matukar maganin tasowar amai ga masu juna biyu ballantana a laulayin watannin farko. Amma kuma akwai bukatar mace mai juna biyu ta tuntubi likita idan tana son shan citta mai yawa.

Muhimman amfanin citta 4 a jikin dan Adam
2. Citta na maganin ciwon mara yayin jinin al’ada
Ciwon mara dai na zuwa ne a kwanakin farko ko kuma kafin wasu matan su fara jinin al’ada. Wannan ciwon marar kuwa na tsananin matsantawa mata tare da hana su sakat.
A wani bincike da aka yi a kan mata 100 masu wannan ciwon marar, an bukace su da su sha citta a lokutan al'adar, kuma ya rage musu wannan ciwon ba kadan ba. Idan mace na son raguwar ciwon mara yayin jinin al’ada, sai a nemi citta a sha ta a shayi mai zafi ko kuma a tauna cittar danya.
3. Citta za ta iya hana dan Adam kamuwa da cutar kansa
Citta na da matukar amfani da masana kimiyya da fasaha ke zaton za ta iya hana dan Adam kamuwa da cutar kansa ko kuma maganinta gaba daya. Wani sinadari mai suna 6-gingerol na iya hana dan Adam kamuwa da cutar kansa. Duk da ba binciken kimiyya da fasaha ne ya tabbatar da hakan ba,, akwai yuwuwar samun maganin kansa a jikin citta.
4. Citta na yin kasa da sikarin da ke cikin jini
Ciwon siga na samun dan Adam ne bayan yawan sikarin da ke cikin jininsa ya wuce misali. Bincike ya nuna cewa citta na dauke da sinadaren da ke rage yawan sikarin cikin jinin dan Adam. Wannan binciken ya tabbatar da cewa citta na da matukar amfani ga masu cutar ciwon sikari.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN