• Labaran yau


  Dogaro da kai: Abin da wata yar yi wa kasa hidima ta yi zai baka mamaki (Hotuna)

  A ko da yaushe, tsarin tafiyar da rayuwar wasu mutane, yakan zama darasi a wajen wasu masu neman hanyar dogaro da kansu. Wata mai yi wa kasa hidima, mai suna Uwaoma Susan Joseph., ta birge mutane bayan ta sayi Keke Napep daga kudin da ta tara, na asusu da ta yi da kudin alawi da ake biyanta, da sauran kudade da take samu wajen fadi-tashi domin ganin ta sami halaliyarta.

  "Ina son in shaida maku cewa idan ka nemi na kanka, kuma ka tashi tsaye, lallai zaka gan sakamako mai kyau" inji Uwaoma.

  "Ana biyana N19,800 a zaman alawus na yi wa kasa hidima, inda nike yi wa kasa hidima suna biyana N20,000 kowane wata, kudaden ne nike ta ajiyewa a asusu, tare da wanda nike kokarin nema daban. Daga karshe dai ko da na kirga, na sami N432,000, wanda na yi amfani da su na sayi Keke Napep, duk da yake ba sabo fil bane, amma na bayar haya a kullum. Na amfana da wannan tsari" cewar Uwaoma.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dogaro da kai: Abin da wata yar yi wa kasa hidima ta yi zai baka mamaki (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama