Bayan shekaru 6 da rasuwar Sheikh Albani, iyalansa sun bayyana halin da suke ciki

Rahotun Legit Hausa

Shekara kwana in ji malam Bahaushe. A cikin watan Fabrairu din nan ne Sheikh Muhammad Auwal Albani Zaria ya cika shekaru shida da rasuwa. Babban masanin hadisin ya rasu ne sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai masa a wata ranar Asabar bayan ya kammala karatu a masallacin Markazus salafiyya da ke Tudun Wada Zaria, a yayin da yake kan hayar komawa gida.

Jaridar Daily Trust ta kai ziyara har gidan marigayin inda ta samu ganawa da babban dansa; Abdurrahman Auwal Albani da kuma wani dan uwansa da ya rike mai suna Mahmud Shu'aib Auwal. Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Abdurrahman ya bayyana cewa marigayin ya rasu ya bar mata uku da kuma 'ya'ya 22.

Marigayin ya rasu ne tare da matarsa guda daya da kuma dansa mai suna Abdullahi Auwal Albani. Kamar yadda Abdurrahman ya bayyana, cibiyoyin karantar da ilimin addinin Musulunci da mahaifinsa ya kafa suna nan suna ci gaba. Kuma a nan ne ake samun abinda iyalansa suke bukatun yau da kullum.

Amma kuma ya ce, babbar matsalar da ake samu a halin yanzu shine na shugabanci a cibiyoyin da mahaifinsa ya bari. Hakan ne kuwa ya shafi hatta ginin Darul Hadith da ake yi wanda ya tsaya tun shekara daya da ta gabata.

Baya ga hakan kuwa, basu da wata matsala. Daga nan jaridar ta tambayi Abdurrahman ko sun ji daga jami'an tsaro bayan da suka yi ikirarin sun kama wasu bata-gari da suke zargi da sa hannunsu a kisan babban malamin. Sai ya ce, "Har yanzu dai shiru kake ji. Basu kira mu ko tuntubar wani makusancinsa ba. Mun jira amma shiru." Mahmud Shu'aib Auwal shima ya koka da yadda jami'an tsaron suka yi sanarwar amma suka yi shiru.

Ya ce dalilin da ya hana su bibiyar lamarin shine biyayya ga wasiyyar mahaifinsu. Muna fatan Allah ya ji kan Sheikh Muhammad Albani Zaria. Ya rahamshesa tare da karbar shahadarsa. Muna fatan Ubangiji ya albarkaci zuri'arsa ya kuma saka ayyukan da yayi wa addinin Musulunci a mizani. Ameen.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN