An kama daraktan kudi da abokan aikinsa guda biyu kan lalata da 'yar shekara 12 a jihar Sokoto

Rahotun Legit Hausa

Hukumar hana fataucin mutane ta kasa a ranar Talata, ta ce ta gurfanar wani daraktan kudi mai shekara 45 a hukumar tsare-tsaren birane da yankuna na jahar Sokoto, Ahmed Yahaya da wasu ma’aikatan hukumar biyu a gaban kotu bisa zargin lalata da wata yarinya yar shekara 12 da ke tallar ruwan leda.

Jami’in labarai na NAPTIP, Mista Vincent Adekoye, a wani jawabi, ya bayyana sauran masu laifin biyu a matsayin mai binciken kudi na gwamnatin jahar Sokoto, Mista Ibrahim Isah mai shekara 46, da mataimaki na musamman ga daraktan kudi, Mista Habibu Abdullahi mai shekara 40.

A cewarsa, hukumar NAPTIP reshen Sokoto ta gurfanar da masu laifin a gaban wata babbar kotun tarayya da ke jahar Sokoto a shari’a mai lamba FHC/7c/2020, Sai dai ya ce ba a riga an ba kowani alkali shari’an ba tukuna.

Adekoye ya ce cikakken bayanin shari’an ya bayyana cewa wani lokaci a Mayun 2019, wacce aka lalatar ta je ofishin wadanda ake zargin don neman taimako na kudi. Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da rashin gatar yarinyar sannan suka yi lalata da ita a lokuta mabanbanta a cikin ofishoshinsu.

Kakakin ya kara da cewa mutum na karshe da yi lalata da yarinyar shine Abdullahi, wanda bayan sanin cewa shugabansa baya nan, sai ya yaudari yarinyar zuwa cikin ofishinsa sannan ya yi lalata da ita, inda ya bata N300 daga bisani.

Ya bayyana cewa hukumar ta kama wadanda ake zargin su uku kimanin makonni uku da suka gabata kan laifukan, bayan hukumar kare hakkin dan adam na kasa, ofishin jahar Sokoto sun tura lamarin zuwa gare su

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN