An amince wa sojojin saman Amurka sa rawani da hijabi

Rahotun Legit Hausa

Rundunar Sojojin Saman Amurka ta yi sauyi a tsarin kayan dakarun ta inda ta bawa musulmi da masu addinin Sikhs daman saka hijabi ko rawani tare da khakin su na soji.

A cewar CNN, sabon tsarin na sojin ya bawa musulmi da masu addinin sikh ikon saka rawani, barin gemu, barin suman kai mai tsawo da hijabi "muddin za a tsaftace shi kuma ya dace da tsari irin na mazan jiya." A baya, Musulmi da masu addinin sikh da ke aikin soja su kan rubuta wasikar izinin neman barin su suyi shiga irin ta addinin su ne daya bayan daya a wasu lokutan.

A kan amince musu da hakan bayan lokaci mai tsawo a mafi yawancin lokuta.A cewar sabon tsarin, zai dauki kwanaki 30 kafin a kammala tabbatar da tsarin ga wadanda ke aiki a Amurka, su kuma kwanaki 60 ga wadanda ke wasu kasashen.

Wannan sabon cigaban na nuna cewa sojojin saman za su samu daman yin addininsu kamar yadda ya dace ba tare da samun tangarda ba yayin aiki. Wasu kungiyoyin kare masu addinin Sikh da musulmi sun ce wannan sabon sauyin da aka yi babban mataki ne wurin kyautatawa masu addinai daban-daban kuma akwai bukatar rundunar sojin ta cigaba da hakan.

Sanarwar da direktan watsa labarai na cibiyar harkokin addinin musulunci na Amurka, Ibrahim Cooper ya fitar ta ce, "Muna goyon bayan sabbin dokokin nan a matsayin wani yunkuri na rungumar jami'an sojojin sama ba tare da la'akari da addinansu ba."

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari