Gwamnatin jihar Kebbi ta ce za ta bar tarihi mai amfani da al'umman jihar Kebbi ba za su taba mantawa da shi ba a fannen kiwon lafiya. Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Babale Umar ne ya ambato haka amadadin Gwamna Atiku Bagudu yayin da yake gabatar da jawabin karshen shekara ga al'umman jihar Kebbi.
ISYAKU.COM ya samo cewa Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya ayyukan alhairi domin aiwatarwa a fadin jihar.
Babale ya bukaci kada matasa su bari yan siyasa su yi amfani da su a matsayin yan daban siyasa, kuma su kaurace wa amfani da magunguna da ababen sa maye da zai gusar da hankalinsu.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari