Yanzu-yanzu: Fashewar gas ta yi sanadiyar rasa rayuka a Kaduna

Raahotun Legit Hausa

Mutane da dama sun rasa rayukan su sakamakon fashewar bututun gas a unguwar sabon tasha da ke Kaduna a safiyar ranar Asabar 4 ga watan Janairu. Lamarin ya faru ne a wani shago da ke kallon gidan man fetur na Total da ke Sabon Tasha a Kaduna.

Karar fashewar bututun gas din ya razana mutane da gidajensu ke kusa da wurin inda su kayi tsamanin fashewar bam ce ko harin Boko Haram. Philip Kambai, daya daga cikin wanda ya tsira daga fashewar bam din ya shaidawa The Cable cewa yana cikin wani shagon aski ne da ke kusa da shagon sayar da gas din tare da wasu mutane uku da suka zo yin aski a lokacin da abin ya faru. Kambai ya ce,

"Ina hanyar fita bayan an gama min aski ne lokacin da na ji kara bum! Na fadi kasa amma na tashi da kyar na haura katanga garin hakan na ji rauni. Wani mutum shima ya haura katangar amma bana tsamanin mai askin da sauran mutane biyun sun fito."

Fashewar gas din ya tarwatsa jikin wadanda suka rasu kamar yadda muka ka jami'an tsaro na tattara sassan jikinsu da ya bazu a titi. An kuma ce fashewar gas din ta yi sanadiyar rasuwar wani mutum da ya ajiye motarsa a gefen titi don ya yi aski a shagon askin da ke kallon shagon gas din.

Shagon da gas ya ke ya kone kurmus amma jami'an kwana-kwana sun yi kokari sun kashe wutar domin kada ta yadu zuwa sauran sassan ginin. Kawo yanzu dai 'yan sanda ba su fitar da sanarwa game da afkuwar lamarin ba a lokacin hada wannan rahoton.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN