Yadda wani masisfaffen zakara ya kashe wani mutum

 Rahotun Legit Hausa

Wani mutum mai shekaru 55 ya rasa ran shi bayan da wata kaza daure da wuka mai kaifi ta soke shi a ciki yayin fada a wata liyafar dare a Indiya. Anyi fadan ne a kauyen Pragadavaram dake Yammacin Godavari a jihar Andhra Pradesh duk da kuwa kotun kolin kasar ta haramta hakan. Mashiryan liyafar sun daura wuka mai kaifi ne a kafar kazar, inji 'yan sanda.

Wanda abun ya ritsa dashi na rike da dabbar ne a hannun shi, yana jiran ya saketa fili don fada. Amma sai kazar tayi kokarin guduwa amma sai wukar ta soki cikin shi wanda hakan yayi ajalin shi. Jaridun yankin sun bayyana sunan mamacin da Saripali Venkateswara Rao mai shekaru 55.

Mutuwar shi kuwa ta zo ne bayan kotun kolin kasar Indiya ta haramta fadan kaji kuma ta bayyana shi a zaluntar dabbobi wanda karantsaye ne ga dokokin hakkokinsu na 1960. Kafin a haramta hakan, mutane 10 sun raunata a kauyen Kavvagunta dake Yammacin Godavari yayin da mutane masu yawa suka raunata a kauyen Chintam Palli sakamakon fadan kaji.

A Indiya, fadan kaji na daga cikin murnar bikin Makar Sankranti, biki ne da ake sadaukar dashi ga ubangiji Surya na ma'abota addinin Hindu. Anyi bikin Makar Sankranti a wannan shekarar ne a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN