Mahaifi ya kunna wuta a al'aurar diyarshi bayan ya daure hannayenta a silin

Rundunar jami'an tsaro na NSCDC a jihar Oyo, sun kama wani mutum da matarsa bisa zargin daure hannayen diyarsu a silin na gidansu, kuma suka kunna wuta a al'aurar diyar tasu mai suna Abibat bisa zargin satan kudi naira N3.000.

Mahaifin Abibat mai suna Taofeek Olawale mai shekara 41, ya ce yana kokarin tsoratar da yarinyar ne sai wutar ta kama rigarta, domin yana zargin ta sace kudin wata makwabciyarsu mai suna Rukayat Trimisiyu.

Ya kara da cewa garin binciken diyarshi Abibat, ya sami N600, daga bisani ta nuna masu inda ta boye ragowar N2400 a cikin gidan..

Matar Taofeek mai suna Romoke, ta ce ta kashe aure tsakaninta da Taofeek tun shekara 7 da suka gabata, kuma bata tare da shi lokacin da ta sami labarin faruwar lamarin.

Kwamandan rundunar NSCDC na jihar Oyo Isikilu Akinsanya, shaida wa manema labarai faruwar lamarin, ya kuma ce Abibat tana jinya a Asibiti.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN