Tap di jan! wata mata ta sayar da mijinta N6000 bayan ta kama shi da wata mata a gadonta

Wani abun mamaki ya faru a kasar Kenya bayan wata mata mai suna Edna Mukwana ta sayar da mijinta a kan kudin kasar Kenya Ksh 1700 wanda ya yi dai dai da N6000 kudin Najeriya domin ta saya wa yaranta tufafin sawa.

Mukwana ta ce ta dauki wannan matakin ne bayan ta kama mijinta wanda ya share kwanaki 7 bai dawo gida ba dumu dumu tare da wata mata a gadonsu na kwanciya.

"Mijina dan giya ne na gaske, kuma mai tsananin neman mata. Na gaya wa matar da ta rudi mijina cewa ta aiko mini Ksh 2000 amma sai ta aiko mani Ksh 1700. Na yi amfani da dukkannin wannan kudin na saya wa yarana tufafin Kirsimeti" inji Mukwana.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

 https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

 SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

 Facebook.com/isyakulabari

 Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN