Soji mafi tsufa a sojin Najeriya da suka yi yakin Duniya na 2 ya mutu, duba shekarunsa

Soja mafi tsufa dan Najeriya a cikin sojojin da suka yi yakin Duniya na II,  Pa Adama Aduku ya mutu ranar Talata yana da shekara 101 a Duniya.

Shelkwatar sojin Najeriya ce ta sanar da haka a shafinta na Twitter.

An haifi Pa Adama Aduku a shekarar 1918, kuma mahaifinsa Abejukolo-Ife karamin manomi ne, wanda ke karamar hukumar Omoha a jihar Kogi. Aduku ya shiga soji a 1945.

A ranar 31 ga watan Disaamba 2018, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kawata Aduku da lambar girma da sojin Najeriya ta bashi.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post