Matashi dan shekara 18 ya yiwa Kakarsa mai shekaru 70 fyade

Eahotun Legit Hausa

Jami'an 'yan sanda a jihar Filato a ranar Juma'a sun kama wani matashi mai shekaru 18 mai suna Marvellous Luka.

Ana zargin matashin ne da yi wa kakar shi mai shekaru 70 fyade, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Dan sandan da al'amarin ke hannun shi, Sifeta Mulleng Alex, ya ce Luka, wanda ke zama a kauyen Dangu-gu da ke karamar hukumar Ampang ta yamma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Dan sandan ya zargi cewa, matashin ya hari kakar tashi ne a dakinta yayin da take bacci. "Sha'awa ce ta kama ni kuma na rasa yadda zanyi da kaina a lokacin. Shiyasa na yanke shawarar kwanciya da ita. Kakata ta dinga kukan neman taimako amma nafi karfinta don haka na yi abinda nake so.

"Tayi kokarin kama ni bayan na gama amma sai na gudu na koma kasuwa inda nake turin baro. Daga nan ne naga wasu mutane sun kama ni tare da mika wa 'yan sanda." In ji wanda ake zargi.

Ya kara da cewa, "aikin shaidan ne kuma ina so kakana da dattawan kauyenmu su yafe min." Mary Samuel, wacce shaida ce a kan abinda ya faru, ta ce taji ihun kakar tana neman taimako amma ita lokacin taje diban ruwa a fanfo ne.

"Na sha mamakin abinda na gani. Nayi kokarin kama shi amma sai ya gudu. Daga nan ne nayi ihu aka bi shi har kasuwa aka kama shi. Na dauki zani wanda ke yashe a kasa na suturta tsohuwar," ta ce.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN