Likitoci biyu, marar lafiya daya sun mutu bayan bullar wata sabuwar cuta a Kano

Rahotun Legit Hausa

A kalla mutane uku da suka hada da likitoci biyu ne suka rasa rayukansu bayan barkewar wata cuta da ake zargin zazzabin Lassa ne a jihar Kano. Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa anyi wa wata mata mai juna biyu aiki don cire yaro daga cikinta a asibitin koyarwa na Malam Aminu da ke Kano.

Matar ta mutu ne sakamakon wani irin zazzabi wanda ake zargin na Lassa ne a makon jiya. Majiyoyi da yawa daga asibitin sun ce likitan da ya taimaka wajen aikin ya rasu bayan kwanaki kadan da mutuwar mai juna biyun.

Hakazalika, wanda yayi wa matar allurai kafin a fara aikin a ICU ya rasu a cikin kwanakin karshen mako. "Baya ga likitocin biyu da suka rasu, babban likitan da yayi wa matar aiki yana kwance rai a hannun Allah. A halin yanzu an ware shi," wani jami'i da ya bukaci ya boye sunansa ya sanar.

"Asibitin koyarwa na Malam Aminu na kokarin samu sinadarin Ribavirin don amfanin duk wadanda suka taba mai juna biyun. Ana bukatar ma'aikatan lafiya da su kiyaye." Mai magana da yawun hukumar asibitin, Hauwa Abdullahi bata dau wayar da jaridar Daily Nigerian ta dinga yi mata. Read more:

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN